TONGUES OF POETRY (ISSUE 5)

TONGUES OF POETRY (ISSUE 5)

WAƘAR GINSHIƘIN ADABI

Ta

 Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA)

Wadda ya yi wa

Dakta Bukar Usman, OON

14571904_1197516576975776_1534011976_o
Dr. Bukar Usman, OON

Jagora: Dakta Bukar na Biu Katibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Alfijir ya keto!!!

Alfijir ya keto ga alamu na waya gari,

Rana idan ta fito tai rabon ayyuka a gari,

Na zam ɗankaɗafi na ɗafe ginshiƙi nagari,

Toro idan ya riƙa shi kaɗai ke kiwo a gari,

Ba ko gwaji zuma da maɗi ko bare sukari,

In Rabbu Ya yarda yanzu ka zam karab da gari,

ALAN Kanawa ne ke yabonka ba alfahari,

Ƙauna da cancanta shi ya sa nake ma shi’iri,

Dakta Bukar na Biu ka zamo gangaren nagari,

Gatan maso adabi a yabonka ba na garari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Farkon mafarina na sako Rabbu kan shi’iri,

Neman amincewar Rabbu ƙarfin cikin sadari,

Jigon zubin waƙa sai ya zam maƙarin gishiri,

Sai warwarar jigo ta sauƙaƙa ya kukan kanari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Mafaka malafata a dogaro ga ƙaunar Bashari,

Mai gargaɗi Bushira kan tafarki na alkhairi,

Shumagaba nagari da ya ida saƙon khairi,

Nurul huda Ɗahe ɗan Amina Sarkin haƙuri.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Jigon zubi na yabo zan yabo ne a gun Bahari,

Fannanu zan wa yabo mai ɗabi’u na alkhairi,

Gishirin miyar adabi Dakta Malam Bukar Bukari,

Jirgin fito a tafi tarakoko nake fahari,

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: A yabon ƙashin bayan adabi sai fa an nazari,

In an karambani makawa babu ai garari,

Ko tuntuɓen baki an ka yo an yiwo garari,

Ni na yi togaciya da Rabbu Allahu Alkabiru.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Sarari gaji da gwani zan yaba wa kyawun ƙudiri,

Mazari uban nazari ga cida mai amo a gari,

Hadari ado a gari alamun zubowar marari,

Dakta Bukar na Biu alƙalam mai karab da gari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Matsalar kiɗan ƙurya yadda ke sa jiki marari.

Haka baitukan waƙa ke sakawa kamar mazari,

Haɗarin ginin baiti ya wuce na baka a kwari,

Ku ji baitukan waƙa na sakawa a yada kwari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Kifi kada a ruwa sun yi ban-ban da ɗan gwadari.

Haka ko ruwan Zam-zam ya yi ban-ban da na tsari,

Tsaran Bukar na Biu ka daɗe kana zaga gari,

Ka gama ka kauce min bai da tamka kakaf a gari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: E!!! Wani na da ilmin nan ya rage shi aiki nagari,

Ilimi da aikinsa shi yake nuna ɗa nagari,

In babu aiki kyau ko ka zamo jaki alfadari,

Masalul himari ka ce yahamilu asfara gari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Wani ga tulin ilimi ba taro darhami da ɗari.

Marashin kwabo da ɗari yaya zai zamo karab da gari,

Wani ga tulin ilimi kana ga ɗan sule da ɗari,

Ba hikima kusfa yaya zai zam kamar Bahari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Wani ya yi rankatakaf ga sani ga kwabo da ɗari,

Kana fagen hikima manihi ne gwanin shi’iri,

A fagen mu’amilla a nan a kai masa shan sukari,

Dakta Bukar na Biu mai hali tarra duk nagari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Rimi ado nagari damina dausayi nagari,

Samji a taka ka yanzu a kwan cikin garari,

Tugi tsiron tsauri ko faƙo ka fito a gari,

Doktoro ɗa na Biu mai halayya ta wa shi’iri.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Yaro nake a tsaye jallabina kawai zikiri,

Sarkin karambani rarrafe ne nake shi’iri,

Ka ji tuntuɓen harshe shekaruna ka yo nazari,

Kar ka hukunta ni rukuni naku Al-Bakari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Kwana a tashi garau safiya zuwa wayi gari,

Da yaro ake babba dare na yi da alfijiri,

Kuna ɗauke sawunku da tafuka naku a sarari,

Muna sanya sawaye namu don kwaikwayo nagari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Mai inkiya da yabo!!!

Al-Aminu ALA nagari!!!

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Mai inkiya da yabo Al-Aminu ALA Bahari, ya

ALAN Kanonmu gari gwaddabe na waƙa shi’iri,

Shi ke kwarara yabo gun Bukar abun alfahari,

Saƙo na yaushe gamo ga shi nan sai a min nazari.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Jagora: Dakta Bukar na Biu Katibi ginshiƙin adabi, ya

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

Amshi: Dakta Bukar na Biu Sahibi ginshiƙin adabi

‘Yan Hausa na ta yabon gudummawarka sashin adabi.

aminu_ladan_abubakarAn haifi Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) a birnin Kano a shekarar 1973. Ya yi karatu har zuwa matakin Diploma a babbar makarantar fasaha ta Kano (SOT) kuma mashahurin mawallafin waƙoƙi ne cikin harshen Hausa. Kaɗan daga mashahuransu sun haɗa da waƙoƙin da ya yi wa marigayi Sarkin Kano Dakta Ado Bayero waɗanda suka haɗa da Bakan Dabo da Mai Martaba da Magajin Dabo. Sannan ya yi wasu waƙoƙi  Bubuƙuwa da Angara da Jami’a da Shahara da sauransu.

Leave a Reply